Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 0:57

[1] Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

[2] Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.

[3] Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo,

[4] yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

[5] yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

[6] Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.

Zabura — Chapters