Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:27

[1] Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!

[2] Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa.

[3] Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.

[4] Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Sela

[5] Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.

[6] Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Da nasara zan rarraba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.

[7] Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Efraim shi ne hular kwanona, Yahuda kuma sandar mulkina.

[8] Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”

[9] Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom?

[10] Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

[11] Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.

[12] Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu.

Zabura — Chapters