Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:16

[1] Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!

[2] Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela

[3] Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

[4] Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

[5] Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

[6] Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

[7] Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye.

[8] Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

Zabura — Chapters