[1] Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah? Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka?
[2] Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa, kabilar gādonka, wadda ka fansa, Dutsen Sihiyona, inda ka zauna.
[3] Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai, dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki.
[4] Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu; suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu.
[5] Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura don yanka itatuwa a kurmi.
[6] Sun ragargaje dukan sassaƙar katako da gatura da kuma gudumarsu.
[7] Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus; suka ƙazantar da mazaunin Sunanka.
[8] Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!” Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar.
[9] Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba; ba sauran annabawan da suka ragu, kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba.
[10] Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah? Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne?
[11] Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama? Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su!
[12] Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa; ka kawo ceto a kan duniya.
[13] Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka; ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye.
[14] Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada.
[15] Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka; ka busar da koguna masu ruwa.
[16] Yini naka ne, dare kuma naka ne; ka kafa rana da wata.
[17] Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya; ka yi rani da damina.
[18] Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji, yadda wawaye suka ɓata sunanka.
[19] Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji; kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba.
[20] Ka kula da alkawarinka, domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar.
[21] Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya; bari matalauta da mabukata su yabe sunanka.
[22] Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka; ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini.
[23] Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka, ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi.