Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:09

[1] Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

[2] Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan, su da aka fansa daga hannun maƙiyi,

[3] su da ya tattara daga ƙasashe, daga gabas da yamma, daga arewa da kudu.

[4] Waɗansu sun yi ta yawo a jejin hamada, ba su sami hanya zuwa birnin da za su zauna ba.

[5] Sun ji yunwa da ƙishirwa, suka kuma fid da zuciya.

[6] Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuma cece su daga damuwarsu.

[7] Ya bishe su ta miƙaƙƙiyar hanya zuwa birnin da za su zauna.

[8] Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,

[9] gama yana shayar da masu ƙishirwa yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.

[10] Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe,

[11] gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka.

[12] Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako.

[13] Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.

[14] Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai ya tsintsinke sarƙoƙinsu.

[15] Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,

[16] gama ya farfashe ƙofofin tagulla ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe.

[17] Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.

[18] Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa.

[19] Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.

[20] Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari.

[21] Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.

[22] Bari su miƙa hadaya ta godiya su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.

[23] Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.

[24] Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.

[25] Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama.

[26] Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.

[27] Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu; suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu.

[28] Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa fitar da su daga damuwarsu.

[29] Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru.

[30] Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.

[31] Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.

[32] Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane su kuma yabe shi cikin taron dattawa.

[33] Ya mai da koguna suka zama hamada, maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa,

[34] ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani, saboda muguntar waɗanda suka zauna a can.

[35] Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu;

[36] a can ya kai mayunwata su yi zama, ya kuma samo birnin da za su zauna.

[37] Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi suka kuma girbe amfani gona;

[38] ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru, bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba.

[39] Sa’an nan yawansu ya ragu, aka kuma ƙasƙantar da su ta wurin danniya, bala’i da kuma baƙin ciki;

[40] shi da yake kawo reni a kan manyan mutane ya sa suka yi ta yawo a cikin jejin da ba hanya.

[41] Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu.

[42] Masu yin gaskiya suka gani suka yi farin ciki amma dukan mugaye suka rufe bakunansu.

[43] Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji.

Zabura — Chapters