Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:08

[1] Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji.

[2] Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma.

[3] Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji.

[4] Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai

[5] Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa,

[6] wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya?

[7] Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;

[8] ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu.

[9] Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.

Zabura — Chapters