Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:24

[1] Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.

[2] Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni.

[3] Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”

[4] Bari waɗanda suke neman raina su sha kunya a kuma kunyatar da su; bari waɗanda suke shirya lalacewata su juya da baya su ruɗe.

[5] Bari su zama kamar yayi a gaban iska, mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu;

[6] bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi, mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu.

[7] Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili kuma babu dalili suka haƙa mini rami,

[8] bari lalaci yă kama su ba zato, bari tarkon da suka ɓoye yă kama su, bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu.

[9] Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangiji in yi kuma murna a cikin cetonsa.

[10] Dukan raina zai ce, “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu, matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”

[11] Shaidu marasa imani sun fito; suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba.

[12] Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta suka bar raina da nadama.

[13] Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,

[14] nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.

[15] Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna; masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba. Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa.

[16] Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a; Suna hararata da ƙiyayya.

[17] Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai? Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu, raina mai daraja daga waɗannan zakoki.

[18] Zan yi godiya cikin taro mai girma; cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.

[19] Kada ka bar maƙaryatan nan, su yi farin ciki a kaina; kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, su ji daɗin baƙin cikina.

[20] Ba sa maganar salama sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar.

[21] Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara! Da idanunmu mun gani.”

[22] Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji.

[23] Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni! Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana.

[24] Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka, Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina.

[25] Kada ka bari su ce wa kansu, “Allah yă ƙara, dā ma abin da mun so ke nan!” Ko su ce, “Mun haɗiye shi.”

[26] Bari dukan waɗanda suke farin ciki a kaina a wahalata su sha kunya su kuma ruɗe; bari dukan waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni su sha kunya da wulaƙanci.

[27] Bari waɗanda suke murna saboda nasarata su yi sowa don farin ciki da murna; bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji, wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.”

[28] Harshena zai yi zancen adalcinka da kuma yabonka dukan yini.

Zabura — Chapters