Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 0:47

[1] Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina.

[2] Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.

[3] Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.

Zabura — Chapters