[1] Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.
[2] Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci; ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.
[3] Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza, ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela
[4] Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.
[5] Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”
[6] Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.
[7] Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.
[8] A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas.
[9] Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,
[10] wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”