Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:30

[1] Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; a gaban “alloli” zan rera yabo.

[2] Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki zan kuma yabi sunanka saboda ƙaunarka da amincinka, saboda ka ɗaukaka a bisa kome sunanka da kuma maganarka.

[3] Sa’ad da na kira, ka amsa mini; ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.

[4] Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji, sa’ad da suka ji maganganun bakinka.

[5] Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.

[6] Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu, amma tun da nesa ya san masu girman kai.

[7] Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala, kana kiyaye raina; ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana, da hannunka na dama ka cece ni.

[8] Ubangiji zai cika manufarsa a kaina; ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada, kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.

Zabura — Chapters