Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:06

[1] Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

[2] Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.

[3] Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

[4] Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.

[5] Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.

[6] Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

Zabura — Chapters