[1] Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata
[2] Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina.
[3] Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna.
[4] Waɗanda suke ƙina ba dalili sun fi gashin kaina yawa; da yawa ne abokan gābana babu dalili, su da suke nema su hallaka ni. An tilasta mini in mayar da abin da ban sata ba.
[5] Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.
[6] Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila.
[7] Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.
[8] Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza;
[9] gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.
[10] Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi dole in jimre da ba’a;
[11] sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya.
[12] Masu zama a ƙofa suna mini ba’a, na zama waƙa a bakin bugaggu da giya.
[13] Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto.
[14] Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye.
[15] Kada ka bar rigyawa yă sha kaina ko zurfafa su haɗiye ni ko rami yă rufe bakinsa a kaina.
[16] Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka; cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.
[17] Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka; ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.
[18] Ka zo kusa ka kuɓutar da ni; ka fanshe ni saboda maƙiyana.
[19] Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka.
[20] Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.
[21] Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi.
[22] Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko; bari yă zama sakamakon laifi da kuma tarko.
[23] Bari idanunsu yă dushe don kada su gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.
[24] Ka kwarara fushinka a kansu; bari fushinka mai zafi yă ci musu.
[25] Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu.
[26] Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni.
[27] Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.
[28] Bari a shafe su sarai daga littafin rai kada a kuma lissafta su tare da adalai.
[29] Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.
[30] Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
[31] Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
[32] Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!
[33] Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.
[34] Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,
[35] gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,
[36] ’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.