[1] Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;
[2] gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.
[3] Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
[4] Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
[5] Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
[6] Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya, gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.
[7] Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
[8] Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.
[9] Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.
[10] A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe; ko ka neme su, ba za a same su ba.
[11] Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama.
[12] Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu;
[13] amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa.
[14] Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke.
[15] Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye.
[16] Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa;
[17] gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.
[18] Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada.
[19] A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace.
[20] Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi.
[21] Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake;
[22] waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su.
[23] In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu;
[24] ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.
[25] Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.
[26] Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka.
[27] Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada.
[28] Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka.
[29] Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada.
[30] Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.
[31] Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi.
[32] Mugaye suna fako suna jira masu adalci, suna ƙoƙari neman ransu;
[33] amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba.
[34] Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.
[35] Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa,
[36] amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba.
[37] Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama.
[38] Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye.
[39] Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala.
[40] Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi.