Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:10

[1] Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.

[2] Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo; don ganewa kalmomi masu zurfi;

[3] don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali, kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;

[4] don sa marar azanci yă yi hankali, yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,

[5] bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora,

[6] don su fahimci karin magana da kuma misalai, kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.

[7] Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.

[8] Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

[9] Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.

[10] Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.

[11] In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;

[12] mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;

[13] za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;

[14] ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”

[15] ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;

[16] gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.

[17] Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!

[18] Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko; ba sa kama kome, sai rayukansu!

[19] Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.

[20] Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;

[21] tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu, tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.

[22] “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi?

[23] Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.

[24] Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,

[25] da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,

[26] Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

[27] sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

[28] “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.

[29] Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

[30] da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

[31] za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

[32] Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;

[33] amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”

Karin Magana — Chapters