Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:03

[1] Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

[2] Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

[3] yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa.

[4] Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya.

[5] Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba.

[6] Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada.

Zabura — Chapters