[1] Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
[2] Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
[3] ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela
[4] Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.
[5] Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.
[6] Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.
[7] Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela
[8] Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.
[9] Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.
[10] “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.”
[11] Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela