Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:36

[1] Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.

[2] Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.

[3] Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,

[4] masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”

[5] “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”

[6] Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai.

[7] Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.

[8] Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.

Zabura — Chapters