[1] Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.
[2] Kyakkyawa ce cikin tsayinta, abin farin cikin dukan duniya. Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona, birnin Babban Sarki.
[3] Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta.
[4] Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare,
[5] sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro.
[6] Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda.
[7] Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.
[8] Yadda muka ji, haka muka gani a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki, a cikin birnin Allahnmu. Allah ya sa ta zauna lafiya har abada. Sela
[9] Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.
[10] Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci.
[11] Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka.
[12] Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta,
[13] ku lura da katangarta da kyau, ku dubi fadodinta, don ku faɗe su ga tsara mai zuwa.
[14] Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.