[1] Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.
[2] Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni.
[3] Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.
[4] Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki.
[5] Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.
[6] Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.”
[7] Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro.
[8] A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai.
[9] “Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka?
[10] Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.”
[11] Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,
[12] don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.