Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:46

[1] Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci; ka saurari kukata. Ka kasa kunne ga addu’ata, ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya.

[2] Bari fiffitawata tă zo daga gare ka; bari idanunka su ga abin da yake daidai.

[3] Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.

[4] Game da ayyukan mutane kuwa, ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina daga hanyoyin tashin hankali.

[5] Sawuna sun kama hanyoyinka ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.

[6] Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini; ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.

[7] Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki, kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu da hannunka na dama.

[8] Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido; ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka

[9] daga mugaye waɗanda suke kai mini hari, daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.

[10] Sun rufe zukatansu marar tausayi, da bakunansu suna magana da fariya.

[11] Sun sa mini ido, yanzu sun kewaye ni, a shirye suke, su jefa ni a ƙasa.

[12] Suna kama da zaki mai yunwan abinci, kamar babban zaki mai fako a maɓuya.

[13] Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su; ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka.

[14] Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so; ’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu.

[15] Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.

Zabura — Chapters