Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:16

[1] Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.

[2] Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.

[3] Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare.

[4] Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.

[5] Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

[6] Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa.

[7] Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.

[8] Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

[9] Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.

[10] Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa, amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.

[11] Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji.

[12] Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,

[13] ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.

[14] Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

[15] Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

[16] fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya.

[17] Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu.

[18] Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

[19] Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

[20] yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.

[21] Mugunta zai kashe mugu; za a hukunta abokan gāban adalai.

[22] Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.

Zabura — Chapters