[1] Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya.
[2] Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa.
[3] Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.
[4] Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.
[5] Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam.
[6] Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.
[7] Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka.
[8] Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya.
[9] Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya.
[10] Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.
[11] Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”
[12] Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.
[13] Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.
[14] Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.
[15] Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.
[16] Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni
[17] sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.
[18] Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.
[19] Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!
[20] Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai.
[21] Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi,
[22] na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.
[23] Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana.
[24] Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.
[25] Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.
[26] Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada.
[27] Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka; kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci.
[28] Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah. Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata; zan yi shelar dukan ayyukanka.