[1] Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka.
[2] Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.
[3] Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.
[4] Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.
[5] Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.
[6] Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,
[7] don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane,
[8] don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,
[9] don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji.