[1] Ka yi mini jinƙai, ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi; dukan yini suna matsa harinsu.
[2] Masu ɓata sunana suna bina dukan yini; da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.
[3] Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.
[4] Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini?
[5] Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni.
[6] Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina.
[7] Sam, kada ka bari su kuɓuce; cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai.
[8] Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?
[9] Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.
[10] Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,
[11] ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?
[12] Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka.
[13] Gama ka cece ni daga mutuwa da kuma ƙafafun daga tuntuɓe, don in yi tafiya a gaban Allah cikin hasken rai.