Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:50

[1] Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma.

[2] Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka.

[3] Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini.

[4] Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina.

[5] Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.

[6] Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai.

[7] A lokacin wahala zan yi kira gare ka, gama za ka amsa mini.

[8] A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji; babu ayyukan da za a kwatanta da naka.

[9] Dukan al’umman da ka yi za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji; za su kawo ɗaukaka ga sunanka.

[10] Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki; kai kaɗai ne Allah.

[11] Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji, zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka; ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba, don in ji tsoron sunanka.

[12] Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata; zan ɗaukaka sunanka har abada.

[13] Gama ƙaunarka da girma take gare ni; kai ka cece ni daga zurfafa, daga mazaunin matattu.

[14] Masu girman kai suna kai mini hari, ya Allah; ƙungiyar marasa imani suna neman raina, mutanen da ba su kula da kai ba.

[15] Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.

[16] Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai; ka ba wa bawanka ƙarfi; ka ceci ni gama na bauta maka yadda mahaifiyata ta yi.

[17] Ka ba ni alamar alherinka, don abokan gābana su gani su kuma sha kunya, gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni.

Zabura — Chapters