[1] Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.
[2] Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.
[3] Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada.
[4] Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.
[5] Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada.
[6] Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.
[7] Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne.
[8] Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.
[9] Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa.
[10] Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo.