[1] Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni.
[2] Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji; da dare na miƙa hannuwa ba gajiya raina kuma ya ƙi yă ta’azantu.
[3] Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi; na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. Sela
[4] ka hana idanuna rufewa; na damu ƙwarai har ba na iya magana.
[5] Na yi tunani kwanakin da suka wuce, shekarun da suka wuce da daɗewa;
[6] na tuna da waƙoƙina da dare. Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani.
[7] “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?
[8] Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?
[9] Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sela
[10] Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.”
[11] Zan tuna da ayyukan Ubangiji; I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā.
[12] Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.
[13] Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne. Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu?
[14] Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai; ka nuna ikonka a cikin mutane.
[15] Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf. Sela
[16] Ruwaye sun gan ka, ya Allah, ruwaye sun gan ka suka firgita; zurfafan gaske sun girgiza.
[17] Gizagizai sun sauko da ruwa, sararin sama suka buga tsawa; kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya.
[18] Aka ji tsawanka a cikin guguwa, walƙiyarka ta haskaka duniya; duniya ta yi rawar jiki ta girgiza.
[19] Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba.
[20] Ka bi da mutanenka kamar garke ta hannun Musa da Haruna.