Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:32

[1] Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina.

[2] Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina.

[3] Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana.

[4] Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.

[5] Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.

[6] Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki; ka koya mini hikima a wuri can ciki.

[7] Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab; ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.

[8] Bari in ji farin ciki da murna; bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.

[9] Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina ka kuma shafe dukan kurakuraina.

[10] Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.

[11] Kada ka fid da ni daga gabanka ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.

[12] Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.

[13] Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka, masu zunubi kuma za su komo gare ka.

[14] Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah, Allahn da ya cece ni, harshena kuwa zai rera adalcinka.

[15] Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, bakina kuwa zai furta yabonka.

[16] Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

[17] Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

[18] Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima.

[19] Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci, hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka; sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka.

Zabura — Chapters