[1] A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
[2] Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.
[3] A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela
[4] Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
[5] Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.
[6] A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
[7] Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
[8] Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
[9] sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela
[10] Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
[11] Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
[12] Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.