Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 0:57

[1] Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini.

[2] Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara.

[3] Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara?

[4] Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.

[5] Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar!

[6] Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.

[7] Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

Zabura — Chapters