Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:14

[1] Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

[2] Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai.

[3] In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya?

[4] Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka.

[5] Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

[6] Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.

[7] Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.

[8] Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.

Zabura — Chapters