Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:14

[1] Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai; daidai ne masu gaskiya su yabe shi.

[2] Ku yabi Ubangiji da garaya; ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.

[3] Ku rera masa sabuwar waƙa; ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.

[4] Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi.

[5] Ubangiji yana ƙaunar adalci duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.

[6] Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.

[7] Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.

[8] Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji; bari dukan mutanen duniya su girmama shi.

[9] Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance; ya umarta, ya kuwa tsaya daram.

[10] Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane.

[11] Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.

[12] Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta, mutanen da ya zaɓa don gādonsa.

[13] Daga sama Ubangiji ya duba ya kuwa ga dukan ’yan adam;

[14] daga mazauninsa yana lura da dukan waɗanda suke zama a duniya,

[15] shi da ya yi zukatan duka, wanda yake kula da kome da suke yi.

[16] Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.

[17] Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.

[18] Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,

[19] don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa.

[20] Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu.

[21] A cikinsa zukatanmu na farin ciki, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.

[22] Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji, ko ma da muke sa begenmu a gare ka.

Zabura — Chapters