[1] Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai.
[2] Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne.
[3] Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.”
[4] Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare.
[5] Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya,
[6] ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane.
[7] An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka.
[8] Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.
[9] Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi.
[10] Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare.
[11] Wa ya san ƙarfin fushinka? Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai.
[12] Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai, don mu sami zuciyar hikima.
[13] Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba? Ka ji tausayin bayinka.
[14] Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu.
[15] Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba, kamar yawan shekarun da muka ga wahala.
[16] Bari a nuna ayyukanka ga bayinka, darajarka ga ’ya’yansu.
[17] Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.