Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:14

[1] Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce,

[2] sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba.

[3] Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.

[4] Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.

[5] Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.

[6] Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma;

[7] da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.

[8] Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”

Zabura — Chapters