Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:27

[1] Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau.

[2] Ubangiji ya duba daga sama a kan ’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah.

[3] Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya.

[4] Masu aikata mugunta za su taɓa koyo. Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?

[5] Ga su, tsoro ya sha kansu, gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai.

[6] Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu.

[7] Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!

Zabura — Chapters