[1] Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.
[2] Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.
[3] Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana.
[4] Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni; rigyawan hallaka sun sha kaina.
[5] Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama.
[6] Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
[7] Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, tussan duwatsu sun girgiza; sun yi rawa domin ya yi fushi.
[8] Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa; wuta mai ci daga bakinsa, garwashi wuta mai ci daga bakinsa.
[9] Ya buɗe sammai ya sauko; baƙaƙen gizagizai suna a ƙarƙashin ƙafafunsa.
[10] Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya; ya yi shawagi a fikafikan iska.
[11] Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi, baƙaƙen gizagizan ruwan sama na sarari,
[12] daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba, da ƙanƙara da kuma walƙiya.
[13] Ubangiji ya yi tsawa daga sama; muryar Mafi Ɗaukaka ya yi kāra.
[14] Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba, walƙiya mai girma ya fafare su.
[15] Kwarin teku sun bayyana tussan duniya sun bayyana a fili sa’ad da ka tsawata, ya Ubangiji, sa’ad da ka numfasa daga hancinka.
[16] Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni; ya ja ni daga zurfin ruwaye.
[17] Ya cece ni daga abokin gābana mai ƙarfi, daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina.
[18] Sun yi arangama da ni a ranar masifa, amma Ubangiji ya zama mai taimakona.
[19] Ya fitar da ni zuwa wuri mai sarari; ya kuɓutar da ni, gama yana jin daɗina.
[20] Ubangiji ya yi haka da ni bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya ba ni lada.
[21] Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi mugunta ta wurin juyewa daga Allahna ba.
[22] Dukan dokokinsa suna a gābana; ban juye daga ƙa’idodinsa ba.
[23] Na kasance marar laifi a gabansa na kuma kiyaye kaina daga zunubi.
[24] Ubangiji ya ba ni lada bisa ga adalcina, bisa ga tsabtan hannuwana a gabansa.
[25] Ga mai aminci ka nuna kanka mai aminci, ga marar laifi ka nuna kanka marar laifi,
[26] ga mai tsabta ka nuna kanka mai tsabta, amma ga karkatacce, ka nuna kanka mai wayo.
[27] Kakan cece mai sauƙinkai amma kakan ƙasƙantar da masu girman kai.
[28] Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci; Allahna ya mai da duhu ya zama haske.
[29] Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna; tare da Allahna zan iya rinjayi katanga.
[30] Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji marar kuskure ne. Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi.
[31] Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba? Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba?
[32] Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya.
[33] Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsaya a kan ƙwanƙoli.
[34] Ya horar da hannuwana don yaƙi; hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
[35] Ka ba ni garkuwar nasara, kuma hannunka na dama yana riƙe ni; ya sunkuya don ka mai da ni mai girma.
[36] Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina, don kada ɗiɗɗigena yă juya.
[37] Na bi abokan gābana na kuma cim musu; ban juya ba sai da na hallaka su.
[38] Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba; sun fāɗi a ƙarƙashin ƙafafuna.
[39] Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi; ka sa abokan gābana suka rusuna mini.
[40] Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu, na kuma hallaka abokan gābana.
[41] Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba.
[42] Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa; na zubar da su kamar laka a tituna.
[43] Ka cece ni daga harin mutane; ka mai da ni kan al’ummai. Mutanen da ban sani ba sun zama bayina,
[44] da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya; baƙi suna rusuna a gabana.
[45] Duk sukan karai; suna zuwa da rawan jiki daga mafakansu.
[46] Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena! Girma ya tabbata ga Allah Mai cetona!
[47] Shi ne Allah mai sāka mini, wanda yake sa al’ummai a ƙarƙashina,
[48] wanda yakan cece ni daga abokan gābana. Ana girmama ka bisa abokan gābana; daga masu tā-da-na-zaune-tsaye ka kuɓutar da ni.
[49] Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji; zan rera yabai ga sunanka.
[50] Yakan ba sarkinsa nasarori; yakan nuna alheri marar ƙarewa ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.