[1] Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana yayinda nake rera ayoyina wa sarki; harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci.
[2] Kai ne mafi kyau cikin mutane an kuma shafe leɓunanka da alheri, da yake Allah ya albarkace ka har abada.
[3] Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi; ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja.
[4] Cikin darajarka ka hau zuwa nasara a madadin gaskiya, tawali’u da adalci; bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki.
[5] Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki; bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka.
[6] Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin; sandar adalci zai zama sandar mulkinka.
[7] Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya sa ka a bisa abokanka ta wurin shafe ka da man farin ciki.
[8] Dukan rigunanka suna ƙanshin turaren mur da na aloyes, da na kashiya; daga kowace fadan da aka yi masa ado da hauren giwa kaɗe-kaɗen tsirkiya kan sa ka murna.
[9] ’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama; a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya.
[10] Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne, Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki.
[11] Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki.
[12] Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki.
[13] Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun; an saƙa rigarta da zaren zinariya.
[14] Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka.
[15] Aka bi da su cikin farin ciki da murna; suka shiga fadan sarki.
[16] ’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka; za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar.
[17] Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai; saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin.