Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:41

[1] Yabi Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.

[2] ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.

[3] Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada.

[4] Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya, mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.

[5] Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.

[6] Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba; za a tuna da mai adalci har abada.

[7] Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.

[8] Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.

[9] Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma.

[10] Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi, zai ciza haƙora yă kuma lalace; sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.

Zabura — Chapters