Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:00

[1] Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

[2] Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.

[3] Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.

[4] Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.

[5] Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,

[6] bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Zabura — Chapters