Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:16

[1] Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela

[2] don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.

[3] Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.

[4] Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela

[5] Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.

[6] Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.

[7] Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.

Zabura — Chapters