Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:02

[1] Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.

[2] Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana.

[3] Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane.

[4] Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai; amincinka ya kai sarari.

[5] A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.

[6] Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.

[7] Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.

[8] Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne; Efraim shi hulan kwanona, Yahuda ne sandana na sarauta.

[9] Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”

[10] Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom?

[11] Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

[12] Ka ba mu taimako a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.

[13] Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu.

Zabura — Chapters