Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 0:58

[1] Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce,

[2] da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana,

[3] sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai;

[4] da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.

[5] Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.

[6] Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.

[7] Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira.

[8] Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.

Zabura — Chapters