[1] Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.
[2] Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina;
[3] gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.
[4] Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya;
[5] na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.
[6] Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,
[7] ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.
[8] Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune.
[9] Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi raina tare da masu son yin kisankai
[10] waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu, waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
[11] Amma na yi rayuwa marar zargi; ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.
[12] Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.