Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:23

[1] Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

[2] Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.”

[3] Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa.

[4] Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

[5] Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,

[6] ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.

[7] Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.

[8] Za ka dai gan da idanunka yadda ake hukunta mugaye.

[9] In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata,

[10] to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.

[11] Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka;

[12] za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.

[13] Za ka taka zaki da gamsheƙa; za ka tattake babban zaki da maciji.

[14] Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.

[15] Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.

[16] Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.”

Zabura — Chapters