[1] Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!
[2] Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga, ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.
[3] Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata, da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;
[4] wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila, farilla ta Allah na Yaƙub.
[5] Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.
[6] Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku; an ’yantar da hannuwansu daga kwando.
[7] Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. Sela
[8] “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!
[9] Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku; ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.
[10] Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.
[11] “Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.
[12] Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu.
[13] “A ce mutanena za su saurare ni, a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,
[14] da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!
[15] Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.
[16] Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”