Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:25

[1] Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici,

[2] masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu suna kuma kawo yaƙi kullum.

[3] Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela

[4] Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.

[5] Masu girman kai sun sa mini tarko; sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu sun kuma shirya mini tarko a hanyata. Sela

[6] Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.” Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji.

[7] Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.

[8] Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji; kada ka bar shirinsu su yi nasara, in ba haka ba za su yi fariya. Sela

[9] Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni su rufu da masifun da leɓunansu suka jawo.

[10] Bari garwashin wuta yă zubo a kansu; bari a jefar da su cikin wuta, cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi.

[11] Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar; bari masifa ta farauci mutane masu rikici.

[12] Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci yana kuma yi wa mabukata adalci.

[13] Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.

Zabura — Chapters