[1] Ya mutanena, ku ji koyarwata; ku saurari kalmomin bakina.
[2] Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā,
[3] abin da muka ji muka kuma sani, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana.
[4] Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
[5] Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu,
[6] don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.
[7] Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa.
[8] Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.
[9] Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna, suka juya da baya a ranar yaƙi;
[10] ba su kiyaye alkawarin Allah ba suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa.
[11] Suka manta da abin da ya aikata, abubuwan banmamakin da ya nuna musu.
[12] Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu a ƙasar Masar, a yankin Zowan.
[13] Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango.
[14] Ya bishe su da girgije da rana da kuma haske daga wuta dukan dare.
[15] Ya tsage duwatsu a cikin hamada ya kuma ba su ruwaye a yalwace kamar tekuna;
[16] ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga ya sa ruwa ya gudu kamar koguna.
[17] Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.
[18] Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi.
[19] Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada?
[20] Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?”
[21] Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,
[22] gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa.
[23] Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sammai;
[24] ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama.
[25] Mutane suka ci burodin mala’iku; ya aika musu dukan abincin da za su iya ci.
[26] Ya saki iskar gabas daga sammai ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa.
[27] Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku.
[28] Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu, ko’ina kewaye da tentunansu.
[29] Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su, gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi.
[30] Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi, kai tun ma yana a bakunansu,
[31] fushin Allah ya ƙuna a kansu; ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu, yana yankan matasan Isra’ila.
[32] Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba.
[33] Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.
[34] A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.
[35] Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.
[36] Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu;
[37] zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa.
[38] Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.
[39] Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa.
[40] Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada suka kuma ɓata masa rai a jeji!
[41] Sau da sau suka riƙa gwada Allah; suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila.
[42] Ba su tuna da ikonsa, a ranar da ya fanshe su daga mai danniya,
[43] ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba.
[44] Ya mai da kogunansu suka zama jini; ba su iya sha daga rafuffuka ba.
[45] Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su, da kwaɗin da suka wahalshe su.
[46] Ya ba da hatsinsu ga fāra, amfanin gonakinsu ga ɗango.
[47] Ya lalace inabinsu da ƙanƙara itatuwan al’ul nasu kuma da jaura.
[48] Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara, tumakinsu ga aradun tsawa.
[49] Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.
[50] Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.
[51] Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham.
[52] Amma ya fitar da mutanensa kamar garke; ya bi da su kamar tumaki ta cikin hamada.
[53] Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro; amma teku ya cinye abokan gābansu.
[54] Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki, zuwa ƙasar tudun da hannunsa na dama ya kame.
[55] Ya kori al’ummai a gabansu ya rarraba ƙasashensu gare su a matsayin gādo; ya zaunar da kabilan Isra’ila a gidajensu.
[56] Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.
[57] Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci, marar tabbas kamar tanƙwararren baka.
[58] Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu.
[59] Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.
[60] Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.
[61] Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.
[62] Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.
[63] Wuta ta cinye matasansu maza, ’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure;
[64] aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.
[65] Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa, kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi.
[66] Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya.
[67] Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba;
[68] amma ya zaɓi kabilar Yahuda, Dutsen Sihiyona, wanda ya ƙaunaci.
[69] Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa, kamar duniyar da ya kafa har abada.
[70] Ya zaɓi Dawuda bawansa ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki;
[71] daga kiwon tumaki ya kawo shi don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub, na Isra’ila gādonsa.
[72] Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya; da hannuwa masu gwaninta ya bi da su.