Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:14

[1] Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.

[2] Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.

[3] Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, Sela

[4] “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”

[5] Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”

[6] Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” Sela

[7] Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”

Zabura — Chapters