[1] Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
[2] Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa,
[3] wanda yake gafarta dukan zunubai yake kuma warkar da dukan cututtuka,
[4] wanda ya fanshi ranka daga rami ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
[5] Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
[6] Ubangiji yana aikata adalci da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne.
[7] Ya sanar da hanyoyinsa wa Musa, ayyukansa ga mutanen Isra’ila.
[8] Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.
[9] Ba zai yi ta zargi ba ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;
[10] ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.
[11] Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;
[12] kamar yadda gabas yake daga yamma, haka ya cire laifofinmu daga gare mu.
[13] Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa, haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;
[14] gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne.
[15] Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona;
[16] iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake.
[17] Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,
[18] tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.
[19] Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama, masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.
[20] Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.
[21] Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama, ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.
[22] Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa ko’ina a mulkinsa. Yabi Ubangiji, ya raina.