[1] Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba amma ga sunanka yă sami ɗaukaka, saboda ƙaunarka da amincinka.
[2] Me ya sa al’ummai suke cewa, “Ina Allahnsu?”
[3] Allahnmu yana a sama; yana yin duk abin da ya ga dama.
[4] Amma gumakansu azurfa da zinariya ne, da hannuwan mutane suka yi.
[5] Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;
[6] suna da kunnuwa, amma ba sa ji, hanci, amma ba sa jin ƙanshi
[7] suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome, ƙafafu, amma ba sa iya tafiya; ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu.
[8] Masu yinsu za su zama kamar su, haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su.
[9] Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
[10] Ya gidan Haruna, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
[11] Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
[12] Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu. Zai albarkace gidan Isra’ila, zai albarkace gidan Haruna,
[13] zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji, manya da ƙanana duka.
[14] Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru, da ku da ’ya’yanku.
[15] Bari Ubangiji yă albarkace ku, shi Mahalicci sama da ƙasa.
[16] Saman sammai na Ubangiji ne, amma ya ba da duniya ga mutum.
[17] Ba matattu ba ne masu yabon Ubangiji, waɗanda suke gangara zuwa wurin da ake shiru;
[18] mu ne masu ɗaukaka Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Yabi Ubangiji.